Duba abinda ya kamata kayi daga zarar antura kudi a asusunka na banki bisa kuskure>>>
Matsaloli daga bangaren banki, ko kuma kuskure daga wajen mutum na isa sabbaba tura kudi asusun wani cikin kure Wani zubin kuma, za ka iya ganin shigowar kudi cikin asusun bankinka daga wanda ba ka tsammani
Kwanakin baya wani mutumi da ya kashe irin wannan kudi ya tsinci kansa cikin Kurkuku Kwanakin baya, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikkin kasa zagon kasa watau EFCC ta gurfanar da wani mutumin da yaki mayar da kudi milyan biyu da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure.
Wannan labari ya yadu ko ina a kasar inda mutane da dama suka bayyana ra'ayoyinsu. Yayinda wasu ke cewa zasu kashe kudin duk da haka, wasu sun ce sun dau darasi kuma ba zasu kashe ba. Hakan ya sa wani masanin harkokin kudi, Yinka Ogunnubi, ya yi kokarin ilmantar da jama'a yadda ya kamata su yi idan aka turo musu kudi cikin kuskure.
If you receive a transfer of any amount into your account and you don't know the source, DO NOT SPEND IT. If you do, you might be at risk of being accused of stealing. Here is what you do:
— Yinka Chukwuemeka Ogunnubi (@yinkanubi) March 9, 2021
1. Notify your bank in writing and ensure it is acknowledged by the bank. https://t.co/1h7RTQnWDb
Yinka ya zayyana abubuwa hudu da ya kamata mutum yayi;
1. Ka sanar da bankinka a rubuce kuma ka tabbatar sun karbi wasikarka
2. Idan sun tabbatar kuskure ne, ta tabbatar da cewa an rubuta hakan tare da lambar asusun wanda yayi kuskuren
3. Idan mai kudin ya tuntubeka kuma ya bukaci ka dawo masa da kudinsa, kada kayi hakan, ka tuntubi bankinka a rubuce domin su tura masa.
4. An fi so ka bukaci bankin ta mayar masa da kanta maimakon kayi da kanka. Saboda ka wanke kanka daga lamarin gaba daya. Ya kara da cewa: "Duk abinda dai za ka yi, kada ka taba kudin."
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Duba abinda ya kamata kayi daga zarar antura kudi a asusunka na banki bisa kuskure>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?