--
Da duminsa: Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano duba dalili

Da duminsa: Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano duba dalili


Wata kotun Majistsare da ke zamanta Gidan Murtala a jihar Kano ta bada umurnin dakatar da mukabalar gwamnatin jihar ta shirya yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar da malaman Kano a ranar Lahadi 7 ga watan Maris, 


BBC ta ruwaito. Alkalin kotun, mai shari'a Muhammadu Jibrin ya yanke hukuncin dakatar da mukabalar sakamakon bukatar da wani lauya mai zaman kasan, Barrister Ma'aruf Yakasai ya shigar wa kotun. 


Yakasai ya bukaci a dakatar da yin mukabalar ne saboda hakan ya saba umurnin da kotu ta bayar a baya na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu da saka karatunsa a kafofin watsa labarai na jihar Kano. 


Mai shigar da karar ya ce bashi daman yin magana yayin mukabalar tamkar watsa karatunsa ne wadda tunda farko aka dakatar da hakan. 


A bangarenta, gwamnatin jihar Kano ta bada tabbacin cewa za ta yi wa kotu biyaya inda kwamishinan sharia na jihar Kano, Barrister Musa Lawan ya sanar da cewa ba za a yi mukabalar da aka shirya yi a ranar Lahadin ba.


Lauyan Barrister Ma'aruf mai suna Barrister Lukman Auwalu Abdullah ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya musu dadi. A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito. 


An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa. JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar 


0 Response to "Da duminsa: Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?