Bazamu halarci zaman mukabala da Abdul-jabbar Ba, - JNI Tayi martani duba abinda tace anan>>>
Kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.
An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.
JNI, ta Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar.
Ta kuma soki 'kalaman batanci' da ake yi ga Manzon Allah da iyalansa da sahabansa cikin wata sanarwa da sakatarenta Khalid Aliyu ya fitar.
"Da farkon lamarin, mun yabawa gwamnatin Kano kan matakin da ta dauka na dakile fitina a kasa da rushewar doka," in ji shi. "Mun kuma sa ran gwamnatin za ta tuntubi mutane da dama kan batun tunda lamari ne da ya shafi kasa baki ko duniya baki daya ba jihar Kano ba."
Kungiyar Jama'atu ta ce bai dace gwamnati da jama'a su bawa Abdul-Jabbar muhimmanci ba duba da abin Allah wadai da ya aikata na batanci da Annabi Muhammadu (SAW). "
Bisa koyarwar mafi yawancin malaman fiqihu, JNI na ganin bai ma dace a yi mukabala da Abdu-Jabbar ba duba da cewa yana yi wa Annabi (SAW) batanci a fili. An san matsayinsa a musulunci; babu bukatar sake bashi dama watsa batancinsa ga duniya.
"Idan da gwamnatin Kano ta tuntubi manyan mutanen da ya kamata domin shirya mukabalar, da an kaucewa fada wa matsalar da aka shiga a yanzu. Don haka, JNI ta ce ba a tuntube ta ba kan matakan da ake dauka kawo yanzu don haka ba za ta hallarci mukabalar ba kuma babu wani sashinta da zai hallarta."
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Bazamu halarci zaman mukabala da Abdul-jabbar Ba, - JNI Tayi martani duba abinda tace anan>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?