Babbar magana: Ba Zan Yarda A Yi Min Rigakafin COVID-19 Ba – Gwamna Yahaya Bello ya bayyana dalilinsa
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya ce ko kadan ba zai amince a yi masa rigakafin cutar COVID-19 ba.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan rigakafin AstraZeneca ya zo Najeriya kuma a daidai lokacin da ake shirin fara rabawa Gwamnoni a ‘yan kwanaki masu zuwa.
Sai dai yayin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Channels a cikin shirinsu na ‘Politics Today’, Gwamnan ya ce ba zai lamunci a yi amfani da mutanen jiharsa wajen gwajin rigakafin ba.
“Ba ruwanmu da cutar Coronavirus a jihar Kogi. Muna da abubuwan da suka fi ta muhimmanci a jiharmu.
“COVID-19 wata ‘yar kankanuwar matsala ce daga cikin matsalolin da muke fuskanta a jihar Kogi; mun sami barkewar annobar zazzabin Lassa da kuma ta Shawara kuma mun magance su ba tare da wani surutu ba.
“Iyakar abin da na sani shine ba na bukatar wata rigakafi, babu abin da yake damu na, lafiya ta kalau. Ba zan yarda ayi min kowacce irin rigakafi ba,” inji Gwamnan.
“Muhammdu Buhari shine Shugaban Kasa kuma ina girmama shi sosai, dukkanmu muna kaunarsa saboda yana shugabanci abin kwaikwayo. Idan yana da bukatar ayi masa rigakafin, abu ne mai kyau, amma ni dai ba zan bari ayi min da mutanen jihata ba” inji Gwamna Yahaya Bello.
A ranar Asabar ne dai ake sa ran yi wa Shugaba Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo rigakafin a bainar jama’a.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Babbar magana: Ba Zan Yarda A Yi Min Rigakafin COVID-19 Ba – Gwamna Yahaya Bello ya bayyana dalilinsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?