--
Ansake kulle makarantu 10 a jihar kwara duba dalili

Ansake kulle makarantu 10 a jihar kwara duba dalili


Ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta soke hukuncinta na sake bude wasu makarantu 10 na jihar inda aka yi rikicin saka hijab. Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar, Kemi Adeosun ta tabbatar, da farko an bukaci makarantun su bude a ranar Litinin amma an soke hakan. 


Ta ce wannan hukuncin an yanke shi ne saboda wasu dalilan tsaro, Premium Times ta wallafa. "A don haka gwamnatin take umartar 'yan makarantun da malamansu da su zauna a gida akasin sanarwar farko da aka yi. 


“Gwamnatin ta mayar da hankali wurin adalci da mutunta doka da hakkokin dukkan 'yan kasa a kowanne lokaci," takardar tace. A watan Fabrairu ne gwamnatin jihar ta bukaci da a rufe wasu makarantu 10 na jihar dake Ilorin har zuwa lokacin da za a shawo kan rikicin saka hijab. 


Makarantun sune: C&S College, ST. Anthony College, ECWA School, Surulere Baptist Secondary School, Bishop Smith Secondary School, CAC Secondary School, St. Barnabas Secondary School, St. John School, St. Williams Secondary School da St. James Secondary School. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Ansake kulle makarantu 10 a jihar kwara duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?