A yanke mata hukuci Kawai a kasheta, Haka Allah yayi Umarni -Inji Mahaifin Amaryar da Kishiyarta ta bankawa wuta ya bukaci hukuma Tayi hakan,
Mahaifin matar da kishiya ta hallaka ta hanyar banka mata wuta ya bukaci hukumomi su tabbatar da cewa an kashe wacce aka kama da wannan laifi. Malam Ibrahim Yayaha Sidi Na Khalifa ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Daily Trust.
Ya ce abinda yake so kawai shine a yanke mata hukuncin da ya kamata. Ya ce a addinin Musulunci, babu laifi idan mutumin da aka zalunta ya zabi daukar fansa saboda Al-Qur'ani ya bayyana hukuncin kisa ba tare da hakki ba. "Ba zan taba yafe jinin diyata ba.
Qur'an yace ' Mun hukunta cewa rai ga rai'.... saboda haka ina son ganin an yanke hukunci kan wadanda suka aikata wannan abin takaicin," Yace. "Ba zan taba yafe musu ba. Ba hadari bane ko kuskure. Ki bugi diyata har lahira, sannan ki bankawa gawarta wuta, ba zan taba yafewa ba."
Rahotanni sun kawo cewa wata mata ta lakadawa kishiyarta dukan tsiya sannan ta cinnawa gawarta wuta.
Kishiyar mai suna Fatima daga yankin Sabuwar Unguwa, garin Katsina, ta yi aure kimanin watanni biyu da suka gabata A cewar wata majiya ta kusa da iyalan, lamarin ya afku ne a ranar Talata "Na ji cewa matar ta je gidan Fatima tare da mutum daya ko biyu," tace “Shakka babu ba da niyan kasheta suka yi ba, amma da suka ga cewa bata numfashi bayan sun yi mata duka, sai suka cinnawa dakinta da gawarta wuta."
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "A yanke mata hukuci Kawai a kasheta, Haka Allah yayi Umarni -Inji Mahaifin Amaryar da Kishiyarta ta bankawa wuta ya bukaci hukuma Tayi hakan,"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?