--
Za'a Aurar da 'yan mata da zawarawa a kano kyauta!

Za'a Aurar da 'yan mata da zawarawa a kano kyauta!


Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da naira miliyan 245 don gudanar da auren mata da yawa a fadin jihar. 


A shekarar 2019 ne gwamnatin jihar ta aurar da mutane 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar. An sanar da hakan ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammed Garba zuwa ga manema labarai a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu. 


Majalisar ta kuma amince da sakin naira miliyan 274.2 ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars domin tafiyar da harkokin kakar wasannin kwallon kafa ta 2020/2021 yadda ya kamata. 


A cewar sanarwar, majalisar zartarwar ta jihar Kanon ta kuma amince da fitar da naira miliyan 29.3 domin aikin allurar rigakafi na shekarar 2020/2021 a tsakanin alumomin makiyaya. An dakatar da shirin tsawon shekaru uku da suka gabata saboda hatsarin kiwon lafiya da asarar tattalin arziki da ke damun wasu al'ummomin jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito. 


Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa majalisar ta amince da sama da naira biliyan 1 da miliyan 200 don kammala aikin gyaran titin Ahmadu Bello Way. Sai kuma naira miliyan 212.9 da aka amince da shi don sake gina dakunan kwanan mata na Dangote a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano da ke Wudil. 


Kukaranta sabbin labarai anan 

https://www.bzglobalservice.com.ng/

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook: 

https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter:

https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Za'a Aurar da 'yan mata da zawarawa a kano kyauta!"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?