--
Yanzu yanzu : An rufe babbar hanyar Benin zuwa Legas yayin da masu zanga-zanga rufe hanya Kalli hotuna

Yanzu yanzu : An rufe babbar hanyar Benin zuwa Legas yayin da masu zanga-zanga rufe hanya Kalli hotuna


Membobin kungiyar Flicthers Association, reshen jihar Ondo sun rufe babbar hanyar Benin-Lagos da ke kan titi saboda zargin badakala da cin zarafin da Gwamnatin Jihar Ogun ta yi.


Jridar dailypost ta rawaito Membobin kungiyar a cikin daruruwan su sun mamaye tare da toshe hanyar Ajibandele na babbar hanyar don nuna rashin amincewa da halin kunci da Gwamnatin jihar Ogun ta jefa su ta hannun jami’anta na kudaden shiga da ke Ayoto.


Tare da masu ababen hawa da matafiya da suka makale a Ajibandele da ke karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, masu tayar da kayar bayan sun kuma koka kan yadda ake bi musu tikitin ba bisa ka’ida ba a Ijebu-Ode jami’an tattara kudaden shiga a jihar Ogun.


Masu zanga-zangar suna dauke da kwalaye masu rubuce rubuce kamar haka “Ya isa wannan fitinar da masu karbar harajin na jihar Ogun,” “Ku daina karbar tikitin Atoyo ba bisa ka’ida ba,” “Ku daina satar manyan motocinmu,“ Ku daina karbar tikitin ba bisa ka’ida ba, ”Ku daina karbar tikitin ba bisa ka’ida ba a Ijebu-Ode a karkashin gada da sauransu.


Yayin da yake ba Gwamnatin Jihar Ogun wa’adin kwanaki 7 don ta kira jami’anta da su ba da umarni, Shugaban kungiyar, Mayegun Oloruntobi ya ce “matakin da aka dauka ba bisa doka ba da kuma cin zarafin mutane” ganganci ne da ake yi wa mambobinsa.


Ya kara da cewa tare da halin da ake ciki na kimanin shekaru hudu, suna karbar tikiti da tarar da ta fara daga N50,000 zuwa N2 million sabanin adadin da aka bayar na N7,000.


A cewarsa, jami'ai a cikin jihar Ogun suna son tursasa su daga harkokin kasuwanci.


A nasa bangaren, sakataren kungiyar, Aro Sunday ya bayyana cewa duk da samun rajistan nasu daga jihar Ondo, Gwamnatin jihar Ondo ba ta taba sanya musu tarar tara ba amma tana amfani da babbar hanyar tarayya wajen karbar su.


Ya kuma roki Gwamna Oluwarotimi Akeredolu da ya kawo musu dauki domin mafi yawan membobin ba za su iya jurewa da halin da ake ciki ba.


Kalli Hotuna a Kasa: 






DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Yanzu yanzu : An rufe babbar hanyar Benin zuwa Legas yayin da masu zanga-zanga rufe hanya Kalli hotuna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?