--
Yanda Jama'ar gari suka cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

Yanda Jama'ar gari suka cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola


Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys' a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa. 


Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito. Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar, DSP, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Yola. 



Nguroje ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:00 na dare. Ya ce an dauki gawar wanda ake zargin ne daga rundunar Jimeta da ke Jimeta. Ya fadawa NAN cewa mambobin kungiyar su uku, suna kan keke ne yayin da suka yi wa matar fashin a hanyar Mubi da ke Jimeta. 


“Matar (an sakaya sunanta) ta yi ihu don neman taimako kuma nan take, wasu fusatattun mutane suka bi wadanda ake zargin, suka kama daya daga cikinsu suka cinna masa wuta. “Sauran 'yan kungiyar biyu kuwa, sun tsere,’’ Nguroje ya fada wa NAN. 


Kukaranta sabbin labarai anan 

https://www.bzglobalservice.com.ng/

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook: 

https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter:

https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Yanda Jama'ar gari suka cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?