
Kalli Bidiyo ‘Yan sanda sun cafke wani mutum da ake zargi da yi wa wata mata fyade da kuma kwakule idanunta a Jihar kudu
Rundunar ‘yan sanda ta cafke mutumin tsirara da ake zargi da aikata laifin fyade da kuma fisge idanun wata mata a jihar Ondo.
Hoton da aka yada a yanar gizo ya nuna yadda wasu gungun mutane suka lakada wa mutumin duka yayin da wanda aka azabtar ya kwanta a kasa a Oluwatuyi, Akure, jihar Ondo (karanta a nan).
Sai da 'yan sanda suka shiga tsakani don hana taron kashe wanda ake zargin ya yi wa fyade.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu ya kara da cewa wanda ake zargi da yi wa fyade da wanda aka yi wa fyaden an kwantar da su a asibitin‘ yan sanda da ke Akure domin yi musu magani.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: bzglobalservicelabari@gmail.com
Allah Ya Kyauta
ReplyDelete