--
'Yan adaidaita sahu: Zirga zirgar ababen hawa ta tsaya Cak a kano duba dalili !

'Yan adaidaita sahu: Zirga zirgar ababen hawa ta tsaya Cak a kano duba dalili !


Fasinjoji a cikin garin kano suna cikin hali mawuyaci biyo bayan fara yajin aikin sai baba tagani da masu keke-napep(adaidaita sahu) suka tsunduma a yau Litinin.


Kungiyar ta shiga yajin aikin ne don kin biyan harajin N100 kullun da gwamnatin jihar ta sanya ta hanyar Hukumar Kula da Hanyoyi da Motoci ta Jihar Kano (KAROTA).

Kungiyar tace, daukan matakin ya zama dole don kauce wa abin da suka bayyana da cewa ana muzguna musu da sunan haraji da sauran tara.


Yawancin titunan cikin birni sun kasance ba kowa sai motoci masu zaman kansu, motocin bus, tasi, babura, da manyan motoci ne kadai suke zurga-zurga.


Wata majiya ta ruwaito cewa mafi yawan matafiya masu matsakaicin hali da ke zuwa wuraren ayyukansu da kuma daliban da ke zuwa makaranta sun koma yin tattaki don isa inda suke gudanar da harkokin su.

DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

1 Response to "'Yan adaidaita sahu: Zirga zirgar ababen hawa ta tsaya Cak a kano duba dalili !"

  1. Agaskiya mulkin da akeyi yanzu a nigeria ba sanin abun daya kamata akan talakan kasa

    ReplyDelete

Tell us what you think about this article?