Ya kamata ace ana saida mai a kan N185 zuwa N200 inji ‘Yan kasuwa
‘Yan kasuwa sun bayyana cewa a yadda kasuwar Duniya ta ke a yanzu, ya kamata farashin PMS watau man fetur ya tashi, idan ba a shigo da tallafi ba. A ranar Litinin, 8 ga Fubrairu, 2021, Punch ta rahoto ‘yan kasuwa su na cewa ya kamata litar man fetur ya rika tashi a kan N185 zuwa N200 a gidajen mai.
Hakan na zuwa ne bayan danyen mai ya kara kudi a kasuwar Duniya, musamman a makon jiya, amma watanni biyu kenan farashin lita bai canza a gida ba. Wasu manyan kungiyoyin ‘yan kasuwa sun yi magana da jaridar, inda su kace wannan karin farashin danyen mai ya sa gwamnati ta dawo da kudin tallafi.
A karshen Disamban bara, ana saida danyen man ‘Brent’ a kan $51.22, kuma gwamnati ta yi ragin N5 a kan lita. Kawo yanzu danyen man kasar ya kara kudi. Daga karin litar fetur da aka yi Nuwamban 2020 zuwa yanzu, gangar danyen man Najeriya ya tashi da 43% a kasuwa; daga $41.51 a lokacin zuwa $59.34 a yau.
A cewar wadannan ‘yan kasuwa, litar man da ake saida wa tsakanin N160 zuwa N165 a gidajen mai a Najeriya, ya kamata yanzu ya kai akalla N185 zuwa N200. Shugaban wata kungiyar ‘yan kasuwa, Mista Clement Isong, ya ce: “Ya danganta da canjin kudi, amma ya kamata kudin lita ya tsaya ne tsakanin N185 da N200.”
“Idan har za a cigaba da saida mai a kan yadda mu ke saida wa, to wani ya na daukar nauyin tallafi, kuma gwamnati ba za ta iya biyan wannan kudi a yanzu ba.” Kamfanin NNPC ta bakin kakakinta, Dr. Kennie Obateru ta musanya batun dawo da tallafin man fetur
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Ya kamata ace ana saida mai a kan N185 zuwa N200 inji ‘Yan kasuwa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?