Wata sabuwa: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa
Wani mutum a Kaduna ya sa jama’a yamutsa gashin baki a shafin soshiyal midiya bayan ya kwato N5,000 da ya aikewa budurwa amma taki zuwa dakinsa kamar yadda suka yi yarjejeniya.
Mutumin ya kai lamarin gaban kotun majistare lokacin da budurwar taki zuwa dakin nasa sannan tayi ta basa uzuri mara kan gado, sai kotun ta umurci bankin budurwar da ya mayar masa da N5,000 dinsa. Bankin yayi kamar yadda kotun ta umurta sannan aka mayarwa da mutumin N5,000 dinsa.
Da yake wallafa labarin a Twitter, shafin @Wizzfarukk ya rubuta: “Wato mutumina ya aikewa wannan budurwa 5k don ta zo dakinsa daga Zaria zuwa Kaduna kawai sai ta fara bayar da wasu uzuri marasa kan gado sannan tayi kokarin yi masa yawo da hankali. “Don takaita labarin kawai sai Baba ya dauki lamarin zuwa kotu sai aka mayar masa da kudinsa bisa umurnin kotu."
Follow me I follow back 💯🙏
— UK Prime Minister 🇳🇬🇬🇧 (@Wizzfarukk) February 4, 2021
Jama’a sun je sashin yin sharhi don bayyana ra’ayinsu.
Ga wasu daga cikin martanin.
@RealTalQ1 ya rubuta: “Wasu lokutan ba wai kudin bane kawai manufar da ke tattare da shi ne. Ta karbi kudi bisa alkawarin kai masa ziyara, sai ta saba yarjejeniya shi kuma mutumin ya nemi a dawo masa da kudinsa...”
@Blackfranchiz ya yi martani: "Wannan gayen sadauki ne."
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Wata sabuwa: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?