Wata matashiyar budurwa ta jefar da jaririyar da ta haifa a Katsina tare da wasiƙa duba dalilinta da abinda ta rubuta a wasikar
Wata Budurwa ta jefar da jaririyar da ta haifa a kan hanya a cikin garin Daura, jihar Katsina tare da rubutun hannu da ke rokon duk wanda ya sami yarinyar ya kula da ita.
An tsinci yarinyar ne a cikin kwali a Unguwar Amare, wani waje ne da garin Daura da misalin karfe 1:20 na safiyar Ranar Juma'a, 12 ga Fabrairu.
A cikin takardar da ta bar wa jaririyar, mahaifiyar ta kuma roki duk wanda ya sami yaron ya sanya mata suna "Barira" Ta kuma nuna nadamarta a kan abin da ta aikata, tana mai cewa wani mutum ne da ba a bayyana sunansa ba ya yaudare ta ya yi mata ciki ya jefar da ita bayan ya yi alkawarin zai aure ta.
A cewar wani mai suna Yawale Musa Kallah Daura, an kawo jaririyar ofishin ‘yan sanda ne ta hanyar masu kirkirar samarda wadanda suka same ta sannan daga baya aka kai ta asibiti.
Ga Bayanin Data rubuta a wasikar:
"ASSALAMU ALAIKUM. INI WANNAN BAIWAR ALLAH DA NA AJE WANNAN JARIRIYA BA DAN SAN RAINA BA ?ADDARA CE, WANI YA YAUDARE NI YA CE ZAI AURE NI YA MIN WANNAN CIKIN YA GUDU YA BARI NA HAIFETA SHI NE NA KAWO TA NA AJIYE TA ALLAH YA HA?A TA DA HANNU NA GARI AMIN, SUNANTA BARIRA ALLAH YA SHIRYI YAN BAYA KUMA ALLAH YA RAYA MANA ITA AMI"
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Wata matashiyar budurwa ta jefar da jaririyar da ta haifa a Katsina tare da wasiƙa duba dalilinta da abinda ta rubuta a wasikar "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?