Update: Gwamnatin Kano ta musanta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara
Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta musanta rushe inda Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ke bayar da karatu da ke kwaryar birnin.
Mai magana da yawun hukumar tsara muhalli ta Kano mai suna KANUPDA, Ado Muhammad Gama, ya shaida wa BBC Hausa cewa duk da yake gine-ginen da aka rusa suna kusa da wurin da malamin yake bayar da karatu amma ba nasa ba ne.
A cewarsa: "Su waɗannan gine-gine wasu mutane ne suka yi su ba bisa ka'ida ba shi ya sa yanzu muka aika aka rusa su.
"A baya, shi Sheik Abduljabbar yana cikin fiye da mutum dubu da suka zo hukumarmu suka ce wajen nasu ne amma sun gaza kawo shaida."
"An bai wa mutanen da suka yi ginin umarnin kar su soma amma suka ki shi ya sa aka rusa yana mai cewa makarantar Sheikh Abduljabbar tana tan babu abin da ya same ta.
Wane fili aka rushe takamaimai?
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnati ta rushe filin Jauful Fara ne wanda Sheikh Abduljabbar ke amfani da shi wurin gudanar da karatukansa.
Sai dai filin makarantarsa mai suna Ashabulkahfi, wanda ya ƙunshi masallaci da gidansa da cibiyar addinin Musulunci, rushewar ba ta shafe su ba.
Da ma dai filin ba wani gini ne a cikinsa ba, kewaye shi aka yi sannan aka saka fitilu domin gudanar da karatu.
Gwamnati ce ta ba ni filin - Abduljabbar
Tun da farko Sheik Abduljabbar ya shaida wa BBC cewa filin nasa ne.
Sai dai wasu mazauna unguwar sun ce filin ana taƙaddama ne a kansa, suna masu cewa ana taƙaddama a kansa
Malamin ya ce gwamnatin tsohon Gwamna Rabi'u Kwankwaso ce ta ba shi filin "amma da baki", sai dai ya yi kokarin karbar takardar amma ba ta fito ba, wanda daga baya ya hakura.
"Amma na ɗauki tsawon shekara 20 ina karatu a wajen," in ji Abduljabbar.
A farkon makon nan ne gwamnatin Abdullahi Ganduje ta haramta wa Sheik Abduljabbar gudanar da wa'azi ko tafsiri saboda kalaman da ta ce yanayi wadanda za su iya tayar da hankali.
Sai dai malamin ya ce zaluntarsa gwamnati ta yi, yana mai ikirarin cewa zai koma yin rubuce-rubuce da za su hana malaman da yake jayayya da su barci.
MAJIYA: BBC HAUSA
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Update: Gwamnatin Kano ta musanta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?