Tap di Jan: Wata mata ta auri kanta da kanta, duba dalili
Wata mata ta yanke shawarar auren kanta bayan ta rabu da saurayinta saura watanni hudu kacal da aurensu.
Meg Taylor Morrison ta ce "eh" ga neman auren kanta a wani kyakkyawan taron da abokai da dangi suka halarta a bikin Halloween na 2020, wanda a ko da yaushe shine burin ranar aurenta.
Matar daga Atlanta, Georgia US, ta rabu da saurayinta a watan Yunin 2020, duk da kasancewar sun yi alkawarin aure ga junansu.
Kwamacala: Wata mata ta rabu da saurayinta ta kuma auri kanta Hoto: MDW features/Geof Krum
A cewar Daily Mail, budurwar mai shekara 35 ta lura da abubuwa da yawa masu kayatarwa game da bikin auren kai kuma ta yanke shawarar ci gaba da ba wa kanta auren da take fata.
Meg ta sarrafa wani kayataccen kek na musamman, ta zabi tufa mai kyau har ma ta sayi zoben aure na lu'u-lu'u wanda a karshe za ta sanyawa kanta.
Babban abin da ke damunta a tunaninta shi ne yadda mutane za su kalle shi kuma idan za su gan ta a matsayin mai son kai ko kuma wata mai kokarin daukar fansar rabuwanta da saurayinta.
Meg ta ci gaba kuma ta gudanar da bikinta a wani waje da ake kira Airbnb a Colorado wanda ya halarci manyan abokai 10 da dangi tare da bin ƙa'idodi na COVID-19.
Ta karanta alkawarinta, ta karɓi zoben bikinta har ma ta sumbaci kanta a cikin madubi.
Meg da baƙinta sun yi liyafa bayan bikin a gidan da ta yi haya kuma suka ci abinci yayin da suke rawa na shagalin bikin.
Ta ce bikin nata nuna soyayya ce don haka ta ji ba ta bukatar wani da za ta aura. Duk wanda ya ji haushi, oho masa.
A wani labarin, Mahaifiyar wasu yara tagwaye a kasar London Kayleigh Okotie tana rayuwa cikin mafarki.
Matashiyar mai shekaru 32 tana matukar alfahari da yadda tagwayenta suke da kyau da kuma yadda babu kama tsakanin jariran biyu.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Tap di Jan: Wata mata ta auri kanta da kanta, duba dalili"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?