Gwamnatin Tarayya ta nada wani sabon shugaban tsaro Duba kaga waye Anan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI )kuma shugaban hukumar leken asirin tsaro na kasa(DIA).
Gwamnatin Najeriya ta sanar da nadin sabon kwamandan tsaron a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu.
Manjo-Janar Samuel Adebayo ya gaji Air Vice Marshal Muhammed Usman, wanda ya yi ritaya daga aikikwanan nan. Sanarwar ta ce:
“Shugaba @ MBuhari ya nada Maj.-Gen. Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI) kuma shugaban hukumar leken asirin tsaro (DIA).
Ya maye gurbin Air Vice Marshal Muhammed Usman, wanda ya yi ritaya daga aiki kwanan nan.”
A gefe guda, majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta bai wa sabbin hafsoshin soji da ya nada wa'adin kawo karshen matsalar tsaro, garkuwar da mutane, 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi kasar nan.
A yayin zantawa da manema labarai a Abuja a jiya, shugaban kwamitin majalisar a kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce idan Buhari ya samar da abubuwan bukata ga sabbin hafsoshin tsaro, ya basu wa'adi a kan aikin da yake so su yi.
Kamar yadda yace, kada gwamnati ta bata lokaci wurin maye gurbinsu da wasu idan suka gaza, Vanguard ta wallafa.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Gwamnatin Tarayya ta nada wani sabon shugaban tsaro Duba kaga waye Anan "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?