--
Shugaban CAN ya baiwa musulmin garin billiri hakuri  mune da laifi injishi,  duba abinda yace

Shugaban CAN ya baiwa musulmin garin billiri hakuri mune da laifi injishi, duba abinda yace


Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, shiyar karamar hukumar Billiri a jihar Gombe, John Joseph, ya bukaci al'ummar Musulman garin su yafe musu bisa rikicin da ya barke a garin makon da ya gabata. 


John Joseph ya bayyana hakan ne ranar Laraba bayan ganawa da gwamnan jihar Gombe, Muhammad Yahaya. 


Daga cikin wadanda ke hallare a zaman sune mataimakin gwamnan, Manassah Jatau; AIG na yan sanda Abubakar Abdullahi; babban Limanin Tangale da shugabar karamar hukumar Billiri, Margaret Bitrus. 


Yayin jawabi ga wadanda ke hallare a zaman, shugaban na CAN ya yi alkawarin aiki da sauran jagororin addinin Kirista dake garin don tabbatar da an yi sulhu. 


"Ga iyayen da suka rasa 'yayansu, muna musu jaje. Mu al'ummar Kirista muna bada hakuri. Muna bada hakuri ga Musulman da aka kona musu Masallaci," Joseph yace. 


Rikicin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi ne wadanda ke zargin gwamnatin da rashin adalci a tsarin zaben sabon Mai Tangale a Billiri. 


Hakanan akwai rikicin addini yayin da aka kona wuraren bautar musulmai a yankin na Billiri. Amma a wani labarin, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar, ya ce tsarin nadin sabon basaraken ya kasance a bayyane, kuma tashin hankalin ya faru ne daga wadanda ke son shafa wa gwamnati bakin fenti don ta zabi wani dan takararsu.


Kafin a a sanar da wanda gwamnan jihar ya zaba, wasu daga cikin mazauna yankin suka fara zanga-zangar nuna su dole a nada musu zabinsu; wanda daga bisani ya jawo tashin hankalin da ya kai ga tsare hanyar Gombe zuwa Adamawa tare kone-konen masallatai da shaguna. Gwaman jihar ta Gombe ya fito yayi bayanin halin da ake ciki tare da bayyana matakin da ya dauka dangane da lamarin. 


SOURCE: LEGIT.NG


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Shugaban CAN ya baiwa musulmin garin billiri hakuri mune da laifi injishi, duba abinda yace"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?