--
Shekau yayi babbar martani gameda da Harin Maiduguri Duba Abinda Yace

Shekau yayi babbar martani gameda da Harin Maiduguri Duba Abinda Yace


Kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya dauka nauyin tashin bama-bamai a Maiduguri a ranar Talata. 


A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin harin da 'yan ta'adda suka kai, ganau suka tabbatar. Wasu mutane 50 sun samu miyagun raunika kamar yadda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar. 


"Ina matukar farin ciki da wannan nasarar da mayakanmu suka samu," Shekau ya sanar a wani bidiyo da Channels TV ta gani. 


Ya kara da musanta cewa sojojin Najeriya sun kwace gonarsa inda yayi tunkaho da cewa yayi nasarar kafa daular Musulunci. 


"Kada ka kira kanka Musulmi saboda kana sallah kuma kana bada zakka. In har ka rungumi al'adun turawan yamma baka cikinmu. Ba za mu taba zama wuri daya ba har sai ka mika wuya ga Allah," yace. 


SOURCE: LEGIT.NG


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Shekau yayi babbar martani gameda da Harin Maiduguri Duba Abinda Yace"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?