
Da duminsa: 'Yan sanda na iya kama ka a ko'ina daga yanzu duba dalili anan
An ba jami’an yan sanda izinin kama duk wani dan Najeriya da yaki sanya takunkumin fuska a taron jama’a Hakan ya biyo bayan sanya hannu a dokar kula da kare kai da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar 26 ga watan Janairu,
Har ila yau, tsarin ya hana taro a wuraren jama’a A yanzu sanya takunkumin fuska a wuraren jama’a a Najeriya ya zama wajibi kamar yadda dokar kariya daga annobar korona ta 2021 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a ranar 26 ga watan Janairu ya nuna.
Sakamakon haka, Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya umurci jami’ansa da su tabbatar da bin tsarin, Kamar yanda Jaridar Legit.ng ta ruwaito.
Da wannan, duk wanda yaki bin umurnin ko yaki sauraron jami’an da ke tursasa dokar na iya fuskantar kamu da hukunci a kotu.
Bugu da kari, laifin na da hukuncinsa a karkashin doka, inda za a ci tarar mutum ko kuma zama a gidan kurkuku na watanni shida ko ma dukka hukuncin biyu kamar yadda yake a sashi na 5 na dokar Killace kai.
Tsarin ya kuma sanya haramci kan taro a wuraren jama’a- wuraren bauta, wurin aiki da makarantu, bankuna, motocin haya, dakunan kwanan dalibai, makarantun kwana, cibiyoyin tsare mutane.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Da duminsa: 'Yan sanda na iya kama ka a ko'ina daga yanzu duba dalili anan"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?