Sabon Rohoton dake shigo mana yanzu haka daga gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara dake gwale kano
An ga jami'an tsaro masu yawa a kusa da gidan Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara a Gwale da ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a safiyar yau Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da shahararren malamin addinin Islama din daga yin wa'azi a jihar saboda salon koyarwarsa da ake ganin yana da matukar tsanani. Gwamnatin jihar ta kuma bayar da umarnin cewa a rufe dukkan makarantun da malamin ke gudanarwa har sai hukumomin tsaro sun gudanar da bincike.
Rahoto ya lura da kimanin motoci biyar na jami'an tsaro masu dauke da manyan makamai, tun daga 'yan sanda zuwa DSS, da jami'an tsaro na NSCDC da sauran wadanda suka kewaye gidan don tabbatar da bin da dokar da aka kafa wa malamin. Su, duk da haka, basu hana mabiya da masu yi masa jaje shiga gidan ba.
Kamar yanda jaridar legit.ng ta rawaito An ga daruruwan mabiya a kewayen gidan da harabar masallacin malamin suna jimami kan matakin Gwamnatin Jihar. Sheikh Abduljabbar, mabiyin darikar Qadiriyya, ana ganin ya samu sabani tsakanin manyan malamai a jihar
Majiya: Legit.ng
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Sabon Rohoton dake shigo mana yanzu haka daga gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara dake gwale kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?