--
Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka

Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka


Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu ranar Alhamis a rikicin da ya barke tsakanin jami'an hukumar Amotekun da wasu Fulani Makiyaya a jihar Ondo. 



Premium Times ta ruwaito cewa wannan rikici ya auku ne a Ago Sanusi, hanyar Uta, karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

 

Majiyoyi sun bayyana cewa gabanin rikicin, makiyayan sun samu matsala da manoma kuma hakan ya sa aka kira jami'an Amotekun. 


A cewar majiyar, yayinda jami'an Amotekun suka isa wajen, makiyayan suka bude musu wuta. Hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani manomi da dan banga. 


"Wani manomi da dan bangan Amotekun sun rasa rayukansu sakamakon harbin da makiyaya sukayi musu a kai," Supo Ojo, wani mazauni ya bayyana. 


Yayinda aka tuntubi Kwamandan Amotekun, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da labarin. "Wasu manoma sun kira Amotekun jiya cewa makiyaya sun kai musu hari kuma jami'anmu suka je wajen don kwantar da kuran. Wani dan banga da manomi sun rasa rayukansu a rikicin," yace. 


Read the latest news here

https://www.bzglobalservice.com.ng/

To download the Bz News24 / 7 news app on your mobile phone, click the text below:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Follow us on our social media pages:

Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

If you have any suggestions or need to let us know, Contact us at: bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?