--
Mukabalar Abduljabbar Da malaman Kano tananan daram - Inji Ganduje

Mukabalar Abduljabbar Da malaman Kano tananan daram - Inji Ganduje


Ana sa ran Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, zai karbi rahoton kwamiti game da shirin muhawarar da ake shirin yi tsakanin Shiekh AbdulJabbar Nasiru Kabara da malaman na Kano,


Kwamishinan harkokin addini na Jihar Kano, Dr. Muhammad Tahir Adamu, ya ce, jama’a ba su fahimci sanarwar makonni biyu da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar a baya ba, “Sanarwar makonni biyun da Gwamnatin ta bayar ita ce kwamitin ya yi aiki a kan shirin tare da gabatarwa ga Gwamna.”


An lura cewa sanarwar da aka fitar a makon da ya gabata ba ta nuna cewa tattaunawar za ta yiwu a yau ba.


Ya kara da cewa, Gwamnan zai yi nazarin rahoton da kwamiti ya gabatar masa tare da sanya ranar tattaunawar.


Dr. Adamu ya ce Gwamnati ba za ta saurari wadannan malaman ba wadanda ke bayar da fatawar tattaunawar.


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Mukabalar Abduljabbar Da malaman Kano tananan daram - Inji Ganduje"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?