Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci nauyin da ke kan shugabannin gargajiya ba, musamman shugaba irin na babbar masarauta irin ta Kano.
Ganduje ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Channels suka yi da shi. Inda suka bukaci sanin dalilan da suka sanya ya tube wa sarkin rawaninsa lokacin yana kan karagar sarautar Kano
A cewar Ganduje, "Tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci rawar da shugabannin gargajiya ya kamata su dinga takawa ba.
"Tabbas tubabben sarkin kullum cikin caccaka da sukar gwamnati yake, kuma ba laifi bane yin hakan saboda kowa yana da damar tofa albarkacin bakinsa. Tabbas mutum ne mai ilimi kwarai. "Bari in baka wani misali, lokacin ina mataimakin gwamna, muna mulkar jihar tare da gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, Sunusi darektan wani banki ne a lokacin. Kuma ya yi wani furuci wanda bai yi wa gwamnati dadi ba.
"A lokacin ya caccaki aikin da gwamnati take yi, inda yace maimakon a samar da ruwa a jihar Kano, muna can muna gina gida a Abuja. Kuma gidan masaukin baki ne amma na gwamnatin jihar Kano ne a Asokoro.
"Ya ce maimakon yadda muke gyara tituna don mutane suji dadin tafiya, mai zai hana mu gina makarantu. Ka ga wannan ai kalubalantar gwamnati yake yi. "A gwamnati kuma ba komai ake tankawa ba, idan kace zaka biye wa mutane toh babu wani abin kirkin da zaka tsinana.
"Gwamnan Kano na lokacin ya bukaci bankin su kori Sunusi ko kuma gwamnati ta cire kudadenta da suke bankin. Bankin basu kore shi ba, don haka gwamnati ta cire kaf dukiyarta da take bankin, a lokacin N969,000,000 ba zan taba mantawa ba," a cewar gwamnan.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to " Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?