
Masu gidan haya sun fatattaki tsohuwar budurwar Dangote saboda bashin kudin haya
Masu gidan haya sun fatattaki tsohuwar budurwar Dangote, Autumn Spikes bayan kwashe wata 6 bata biya kudi ba Kamar yadda aka gano, ta gaza biyan kudin hayan tun daga watan Maris zuwa Augusta na shekarar da ta gabata
An gano cewa Spikes da Dangote sun kwashe kusan shekaru 10 suna zuba soyayya kafin su rabu dutse a hannun riga Duk da soyayya da Aliko Dangote, bakar fata da yafi kowa kudi a duniya, masu gidan haya a arewacin Miami da ke florida sun fatattaki Autumn Spikes sakamakon kasa biyan kudin haya na watanni shida da tayi.
Kamar yadda Premium Times ta gano, Spikes da Dangote sun yi soyayyar sirri na kusan shekaru 10 kafin daga bisani su rabu dutse a hannun riga.
Amma ko a lokacin da alakar ke nan lafiya kalau, Spikes ta tara kudin haya har $13,230 daga watan Maris zuwa Augustan 2020, takardun kotun da jaridar Premiuum Times ta gani ya bayyana.
Mamallakin gidan, The Shoreline dake SoleMia, 2301 Laguna Circle, North Miami, Florida ya bai wa Spikes wa'adin kwana 30 a kan ta biya ko kuma ta tashi. a ranar 5 ga watan Augusta. Spikes bata biya ba kuma bata tashi daga gidan ba mai lamba 1708.
Bayan karewar wa'adin kwanaki 30 din a ranar 19 ga watan Satumban 2020, an maka ta a kotun yankin Miami Dade da ke Florida, kotun da Dangote ya maka ta a watan Janairun da ta gabata. Tun a wancan lokacin, an yi ta kokarin samun Spikes domin bata sammaci amma hakan ya faskara.
Daga bisani mai gidan hayan ya bukaci kotun da ta saurari karar ta bangarensa, wanda kuma hakan ta kasance. Kotun ta yanke hukuncin a fitar mata da kayanta cikin sa'o'i 24 amma kafin nan sai aka tarar har ta kwashe kayanta da kanta.
MAJIYA: LEGIT
Read the latest news here
https://www.bzglobalservice.com.ng/
To download the Bz News24 / 7 news app on your mobile phone, click the text below:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Follow us on our social media pages:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
If you have any suggestions or need to let us know, Contact us at: bzglobalservicelabari@gmail.com
to idan gaskene to sai muce allah ya kyauta
ReplyDeleteHi
ReplyDelete