--
Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa

Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa



A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da kashe Naira biliyan 11.3 (11,352,457,101.70) a matsayin kasafin kudin Asusun Dogaro na ’Yan sandan Nijeriya (NPTF) na kasafin kudin shekarar 2020. 


Kimanin N1.3bn (1,362,814,243) daga cikin kudin da aka kasafta domin siyan barkonon tsohuwa. An ware kimanin Naira biliyan daya domin sayen makamai da alburusai, Premium Times ta kawo. 



Amincewar ta biyo bayan la'akari da daukar rahoton da ya dace na kwamitin majalisar dattijai da na wakilai kan harkokin 'yan sanda. Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Haliru Jika ne ya gabatar da rahoton.


Amincewar majalisar dattijan na zuwa ne mako guda bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura kasafin kudin ga majalisar dattawan domin dubawa da kuma amincewa. Aiwatar da kasafin kudin zai fara a ranar 30 ga Afrilu, 2021. 


Mista Jika a jawabinsa ya ce wannan shi ne kasafin farko na NPTF, tun lokacin da aka kafa dokar a shekarar 2019. 


Kashi 0.5 cikin 100% na yawan kuɗaɗen shiga da aka samu a Asusun Tarayya da kuma 0.5% cikin 100% na adadin Haraji da aka tura su zuwa asusun NPTF; sauran hanyoyin samun kudin shiga kamar yadda aka tsara a dokar NPTF ba su kawo kudi ba, in ji shi. 



Da yake bayar da bayanin rarar bangaren kasafin kudin, dan majalisar ya ce ana sa ran kudin Shiga Naira biliyan 35 (N34,984,314,243) yayin da aka ware Naira biliyan 11.3 (N11,354,457,101.70) don kashewa hidimar. 


Ya bayyana cewa ragowar N23.6 biliyan (N23,631,857,141.30) na 2020 za a kwashe su zuwa kasafin 2021 na NPTF. 


Don haka, ya yi kira ga NPTF da ta hanzarta aiki kan aiwatar da kasafin kudin 2020 domin cimma wa'adin 30 ga Afrilu. A jawabinsa, 



Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce amincewa da kasafin na NPTF zai “taimaka wa 'yan sanda su kara karfinsu kuma ba shakka, zasu samar da ingantattu da nagartattun ayyuka a duk fadin kasar.”


"Wannan na daga cikin fa'idodin abin da muka tattauna a nan - Asusun Amintattun 'Yan Sanda - kuma na tabbata cewa Majalisar Dokoki ta Kasa za ta ci gaba da tallafa wa jami'an tsaronmu don kyakkyawan aiki," in ji shi. 


SOURCE: LEGIT.NG


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?