--
Tirkashi: Kyawunta yayi sanadin sallamarta daga gurin aiki

Tirkashi: Kyawunta yayi sanadin sallamarta daga gurin aiki


An umurci wata tsohuwar sarauniyar kyau ta yi murabus daga aikinta a asibiti saboda 'kyan ta ya yi yawa' kamar yadda LIB ta ruwaito. 


An nada Claudia Ardelean, mai shekaru 27 ta yi aiki a kwamitin asibitin Pneumophthisiology Clinical Hospital a kasar Romania duk da cewa ba za a rika biyanta albashi ba. 


Ardelean tana da digiri biyu a aikin lauya da nazarin al'adun turawa. Bayan samun aikin, ta yi farin ciki har ta wallafa a kafar sada zumunta a ranar 8 ga watan Fabarairu. 


Tsohuwar sarauniyar kyan ta wallafa hoton selfie da ta dauka a gaban ginin asibitin inda ta rubuta: "Ina godiya saboda gudunmawa da amintaka da na samu daga Cluj Nationtal Liberal Party!". 


Sai dai bayan hakan, wasu suka fara sukar ta suna cewa ta samu aikin ne kawai saboda kyau da ta ke da shi. Newspaper Click ya ce sakamakon sukar da aka yi mata, an tilasta mata yin murabusa saboda tana da "kyau da yawa". 


Claudia wacce yanzu ta ke aiki a matsayin lauya a wani kamfanin kasar ba ta yi tsokaci game da ajiye aikinta na kwamitin asibitin ba. 


Shugaban Cluj Alin Tise ta amsa cewa ta cancani amma duk da hakan ta fitar da sanarwa cewa, "na yi nadamar abinda ya faru. "Na bukaci Claudia Ardelean ta yi murabus." 


Kukaranta sabbin labarai anan 

https://www.bzglobalservice.com.ng/

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Tirkashi: Kyawunta yayi sanadin sallamarta daga gurin aiki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?