Ku kalli yanda Mabarata a jihar Jigawa suka hana gwamna fita daga cikin gidansa
Wasu gungun mabarata da galibinsu mata ne, sun yiwa gidan gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar kawanya. Sun nemi kuɗi, suna cewa suna jin yunwa, The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya je Babura ne, mahaifar kasarsa, don sake jaddada zamansa mamba a jam’iyyar APC a mazabarsa da ke Kofar Arewa Primary School. Nan da nan ya shiga harabar gidansa bayan da ya sake jaddada rajistar jam'iyyarsa a garinsu, mabaratan suka kewaye gidansa.
An yi zargin cewa wata 'yar karamar hasuma ta faru lokacin da mabaratan suka kewaye gidan gwamnan suna neman a basu kudi, kuma sun bayyana cewa rayuwa na yi musu kunci. Mabaratan sun taru a gidan gwamnan domin ya saurare su. Amma bai samu fitowa ba.
Matsala ta fara ne a lokacin da mabaratan suka dade a waje suna jiransa ba tare da wata alama da ke nuna cewa gwamnan zai saurare su . Madadin haka, sai jami'an tsaro ke kokarin tarwatsa su.
Sun fara ihu kuma sun dauki hanyar shiga harabar. Su dubbunsu, sun ƙi barin wajen, yayin da suka ingiza jami'an tsaron cikin gidan kuma suka kulle duk hanyoyin shiga gidan gwamnan.
Lamarin ya sanya manyan mutane da yawa rashin samun damar zuwa gidan gwamnan, ciki har da ‘yan jarida, wadanda aka tilasta su ja da baya saboda tsoron kada gungun mutanen su far masu.
Daya daga cikin matan da suka yi garkuwar da gwamnan a gidansa, Malama Halima Hadi ta ce matsalar su ba COVID-19 ba ne, duk da cewa ta ce akwai batun talauci, rashin aikin yi, da fyade da ke addabar su. Ta kuma ce mutane ba sa iya samun cin abinci sau uku a rana.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Ku kalli yanda Mabarata a jihar Jigawa suka hana gwamna fita daga cikin gidansa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?