--
Kamfanin WhatsApp Ya sanar da hukuncin dazai dauka akan wadanda basu amince da sabbin manufofinsu ba, duba hukuncin anan>>>>

Kamfanin WhatsApp Ya sanar da hukuncin dazai dauka akan wadanda basu amince da sabbin manufofinsu ba, duba hukuncin anan>>>>


Kamfanin manhajar sadarwa na WhatsApp mallakar Facebook ta sanar da hukuncin da za ta yi wa masu amfani da manhajar da suka ƙi amincewa da sabbin tsare-tsaren da ta ɓullo da su. 


Kamar yadda ya ke a bayanin da ke shafin intanet na kamfanin, an bawa masu amfani da manhajar da ba su amince da sabbin tsarin ba zuwa ranar 15 ga watan Mayu su yi hakan ko kuma nasu ya dena aiki, rahoton The Nation. 


Waɗanda hakan ta faru da su ba za su iya karanta saƙo ba a manhajar, a cewar kamfanin amma za su iya amsa kira kuma za su iya ganin alamar shigowar sabbin saƙonni amma hakan ma 'na gajeren lokaci'. 


A hirar da aka yi da TechCrunch, kamfanin ya ce 'gajeren lokacin' zai kasance na makonni kafin a rufe shafinsu a ranar 15 a ga watan Mayu. 


Masu amfani da manhajar na iya rasa saƙonnin su duba da cewa dokokin WhatsApp na wadanda suka dena amfani da manhajar ya ce "a kan goge saƙonni bayan kwana 120 sun shuɗe ba a yi amfani da manhajar ba".


Idan za a iya tunawa, a watan Janairu kamfanin ta fasaha ta sanar da cewa za ta aiwatar da canjin daga ranar 8 ga watan Fabrairun 2021. 


Kamfanin ta jinkirta zartar da sabbin tsare-tsaren da watanni uku sakamakon damuwa da wasu masu amfani suka nuna kan yiwuwar bayanansu za su iya komawa shafin Facebook, wacce ita ke da WhatsApp.


Duk da cewa WhatsApp na iya ganin bayanai kamar lambobin wayar masu amfani da WhatsApp tun 2016, kamfanin ya tabbatar cewa


"WhatsApp baya iya karanta saƙonnin ku domin akwai fasahar da ke kare hakan ta yadda masu saƙon kawai za su iya karanta abinsu." 


WhatsApp ta ce wannan sabon tsarin zai bawa masu kasuwanci damar iya biyan kuɗi cikin sauƙi ne, a cewar TechCrunch. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Kamfanin WhatsApp Ya sanar da hukuncin dazai dauka akan wadanda basu amince da sabbin manufofinsu ba, duba hukuncin anan>>>>"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?