Kalli Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa
Dakarun sojoji na Operation Safe Haven, OPSH, sun kama wani da ake zargin shugaban masu garkuwa ne, Adamu Umar, da ake zargin ya sace wata mata a jihar Plateau.
Kwamandan OPSH, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo, wanda ya yi holen wadanda ake zargin a ranar Juma'a, ya ce Umar ya yi wa wata mata, Zuwaria Mohammed dabara ya kai ta Guratop a karamar hukuma Jos ta Arewa da sunan akwai kayan da zai sayar mata da su.
Bayan ta isa wurin sai ya tsare ta, ya tuntubi mijin ta, Rabiu Mohammed ya nemi a biya shi kudin fansa Naira miliyan 2 kafin ya sako ta. Mijin matar ya yi korafi ga OPSH inda suka bashi shawarar ya amince zai biya kudin fansar.
"Mijin ya yi korafi zuwa ofishin OPSH inda suka bashi shawarar ya amince zai biya kudin fansa sannan aka amince da inda za a karbi kudin. Sojojin OPSH suka yi kwantar bauna a wurin da za a karbi kudin suka kama mai garkuwar suka ceto matar," in ji kwamandan.
Kwamandan ya kara da cewa an taba kama mai garkuwar sau biyu a baya kuma yana cikin jerin sunayen wadanda yan sanda ke nema ruwa a jallo saboda garkuwa.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kalli Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?