Kalli Bidiyon wata yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda
Bidiyon wata matashiyar yarinya tana yakar 'yan fashi da makami wadanda suka shiga shagonsu suna barazana ga mahaifiyarta ya karade kafafen sada zumuntar zamani.
Mummunan lamarin ya faru ne a yankin Uribe Uribe da ke Bagota, babban birnin Colombia a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu lokacin da wani a babur ya tsaya a shagon sannan ya kutsa ciki da karfe 4am.
Mai shagon tana da yara mata biyu masu shekaru biyu da 14 kuma suna cikin shagon a yayin da dan fashin ya kai harin, The Nation ta wallafa.
Bidiyon lamarin wanda CCTV ta cikin shagon ta nada ya nuna wani mutum sanye da bakaken kaya da kuma bakar malfa, ya shiga shagon inda ya nufa wurin karbar kudi. Zakakura kuma jarumar yarinyar an ganta ta fuskanci dan fashin inda take masa barazana tare da nuna masa adda.
Ta wurga addar a iska inda hakan yasa dan fashin yayi hanyar gaban shagon domin arcewa. Wani dan fashin ya bayyana a cikin shagon don taimakon dan uwansa amma ta fatattakesu inda su biyun suka bar shagon tare da hayewa babur dinsu suka karawa bujensu iska.
Kamar yadda rahotannin suka bayyana, wadanda ake zargin sun harba mahaifiyar yarinyar kafin su bar shagon. An gaggauta mika ta asibiti inda aka samu shawo kan matsalar babu bata lokaci.
KU LATSA HOTON DAKE QASA DOMIN KU KALLI BIDIYON:
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kalli Bidiyon wata yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?