--
Kalli bidiyon hatsarin jirgin ƙasa da trela a Legas Latsa nan

Kalli bidiyon hatsarin jirgin ƙasa da trela a Legas Latsa nan


Jirgin kasa ya yi da karo da babban mota (trela) makare da abincin dabobi a Iju-Ishaga, layin Jonathan Coker a karamar hukumar Ifako-Ijaiye da ke jihar Legas, The Cable ta ruwaito. Shaidun ganin ido sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa babbar motar ta kuma murkushe wata a dai-daita sahu. 


Jami'an tsaro a halin yanzu suna can suna kokarin ganin al'amurra sun daidaita a wurin da hatsarin ya faru misalin karfe 8.52 na safiyar yau. 


Hatsarin ya janyo cinkoson ababen hawa a yankin hakan yasa ake bawa masu ababen hawa shawarar sun sauya hanya. A lokacin da ake hada wannan rahoton, babu wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin. Dreban a dai-daita sahun ya tsira da ransa. 


Ga bidiyon a kasa: 


0 Response to "Kalli bidiyon hatsarin jirgin ƙasa da trela a Legas Latsa nan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?