Kalli bidiyon jawabin Malam Abduljabbar nasiru kabara da yayi yanzu
Sheikh AbdulJabbar Sheikh Nasir Kabara ya bayyana dakatarwar da gwamanatin Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".
Shiekh Abduljabbar ya faɗa wa BBC HAUSA cewa duk da ita gwamnati da kanta, ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar, ta tabbatar da abin da ake yi masa zalunci ne, amma ta dakatar da shi ba tare da ba shi damar kare kansa ba.
Abduljabbar dai na waannan kalami ne biyo bayan rufe makarantarsa da masallacinsa da gwamantin Kano ta sanar da yi a ranar Laraba tare da haramta saka karatunsa a kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai a jihar.
Shehin malamin ya ce taron da ya gudanar a makon da ya gabata na daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin, ganin cewar duk yunƙurin hana taron ya ci tura.
"Kwamishinan ilimi ya faɗa da yawun gwamnati cewa ana zaluntar Abduljabbar ne kuma abubuwan da malaman nan suke yi ba su da gaskiya ko kaɗan, sun shigar da siyasa ne cikin addini," in ji shehin malamin.
"A matsyaina na wanda ba kowan kowa ba, kamar kwamishinan ilimi ya ce ana zaluntar Abduljabbar, ai ya isa raddi ga gwamnati cewa abin da ta yi zalunci ne.
"Kuma ta yi wannan kalaman ne kan abin da waɗannan azzaluman da suka tabbata cewa su azzalumai ne, sun sauka daga kan layin ilimi suna amfani da siyasa da gwamnati wajen cimma wata manufa wadda suka kasa cimmawa a ilimance.
"AIG (mataimakin sufeto janar na 'yan sanda) ya aiko mani da takarda cewa 'yan Izala sun kawo ma takardar muƙabala, na ce masa ni ba a yi haka da ni ba. Sai ranar Litinin da ta wuce sai ya turo ya ga takardar an sako ta tagar masallaci - ba hannu da hannu ba.
"Da na duba sai na ga takardar da 'yan Izala suka ce sun ba ni ce, take na kira AIG na ce masa tabbas mutumin da ya ce mun yi muƙabala da shi gaskiya ne amma sauya suna ya yi, kuma na ce masa ya faɗa wa gwamnati a shirya muƙabala.
"Kawai sai na ji sanarwa jiya an ce an hana ni yin karatu ba tare da an tattauna komai ba, duk da na ce wanda aka zaɓa zan zauna da shi."
Da BBC ta tambaye shi game da zargin yin kalaman ɓatanci ga sahabbai, Abduljabbar ya ce ba a zauna da shi ba balle a tabbatar yana zagin sahabban.
Duk da cewa malamin wanda ya sha tayar da ƙura game da wasu al'amura na addinin Musulunci, ya ce zai yi biyayya ga umarnin rufe wurin karatu, sai dai ya yi kira ga mutane da su yi amfani da katin zaɓensu wurin sauya gwamnati tare da yi wa masu sukarsa "baƙin albishir".
"Shawarar da nake bayarwa ita ce mutane su tanadi katin zaɓensu domin kawo gwamnatin da za ta yi mana adalci. Mutane su karkaɗe katin zaɓensu, wanda ba shi da shi ya je ya yi.
"Manufata ita ce mu samu ɗan takarar da zai yi mana adalci, mu yi alƙawari da shi, jama'a su yi masa ruwa ƙuri'a, ya tabbatar mana da adalci. Da ma amfanin dimokuraɗiyya kenan - wanda bai yi maka ba ka cire shi ka kawo wani."
"Zan bi umarnin, an ma rufe su. Sai dai ina yi musu baƙin albishir, rubuce-rubuce na nan tafe. Sai dai in an yi dokar shi ma rubutun a hana ni, amma rubutun da zai hana su barci yana nan in Allah ya yarda."
KALLI BIDIYON HIRARSA DA BBC HAUSA:
Majiya: BBC HAUSA
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kalli bidiyon jawabin Malam Abduljabbar nasiru kabara da yayi yanzu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?