--
Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar - Inji Lauyan sa, Duba abinda yace

Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar - Inji Lauyan sa, Duba abinda yace


Barista Rabiu Shuaibu Abdullahi, Lauyan Malamin addinin Musulunci da ke Kano, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara, ya yi korafi akan Kalaman gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. A cewar Lauyan, kalaman Ganduje suna da hatsari ga zaman lafiya da rayuwar Sheikh Kabara. 


A yayin da yake tattaunawa da jaridar Daily Trust, Barista Rabiu, ya bayyana cewa, "mutumin da nake karewa ba ya fuskantar barazana daga wurin kowa sai daga wurin gwamnatin da ya kamata ta bashi kariya. 


"Ku je ku saurari maganganun da gwamna ya yi yayin ganawarsa da limaman Jihar Kano a ranar Alhamis din da ta gabata, ya basu umarnin akan abinda da zasu fada yayin hudubar Sallar Juma'a. Ya bukaci su tunzura jama'a akan Abduljabar tare da tura jami'an tsaro su kuma bashi kariya. 


"Idan kai ne zaka yarda da jami'an tsaron? Ta yaya mai sukar lamuranka zai yi ikirarin cewa zai baka kariya. Shi yasa bama ganin barazana daga wani bangare sai daga Kalaman gwamna," a cewarsa. 


Da aka tambaye shi ko yana ganin gwamna Ganduje yana son daukar fansa ne akan Malamin saboda rashin goyon bayansa a zaben 2019, sai ya ce, "me yasa bai dauki mataki akansa a wancan lokacin ba? Me yasa sai yanzu? wannan magana ce ta harkar addini ba siyasa ba.


"Bai kamata ya fake da kungiyar Malaman addini domin daukan fansar abinda ya shafi siyasa ba. Shi shugaba kamata ya yi ace yana da yalwar zuciyar da zai jure abubuwan da na kasa da shi suka yi masa. Dole ne sai ya dauki fansa?" Lauyan ya tambaya. 


Kukaranta sabbin labarai anan 

https://www.bzglobalservice.com.ng/

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar - Inji Lauyan sa, Duba abinda yace"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?