Kada kuyi Muqabala da Abdul-jabbar - Kiran Dr. Ahmad Gumi ga Malaman Jihar Kano da gwamnati Kalli Bidiyo anan>>>
Babban malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa game da sabanin da aka samu da Abduljabbar Nasiru Kabara.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya fito ya yi kira ga gwamnatin Kano da malaman Ahul-Sunnah da su guji yin mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da wani karatun fiqihu a garin Kaduna.
A wannan bidiyo da ya shigo hannunmu,
malamin ya bada shawarwari uku da yake ganin za su yi wa gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje da malaman jihar Kano amfani.Part 2 pic.twitter.com/usSjnYmrx2
— I Z A L A (@el_uthmaan) February 13, 2021
Ahmad Abubakar Gumi ya jefi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da rigar shi’a, ya ce don haka ba za a taba samun matsaya tsakaninsa da sauran malaman Kano ba.
A ra’ayin Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ba za a iya cin ma madogararar da za a tattauna a kai, tsakanin masu da’awar Ahlul-Sunnah, da malamin da ke bin shi’a ba.
Gumi ya bayyana cewa a karshen wannan zama, sauran gama-garin al’umma ba za su iya gane mai gaskiya tsakanin Abduljabbar Kabara da ragowar malaman ba.
Shehin ya yabi mahaifin wannan malami, Sheikh Nasiru Kabara, wanda a cewarsa ya zo har masallacin Sultan Bello, ya yaba da koyarwar Marigayi Ahmad Gumi.
Ahmad Gumi ya bayyana cewa akwai abin da Abduljabbar Nasiru Kabara yake nufi a zuciyarsa, ya yi masa addu’a, kuma ya bada shawarar rufe taba hadisan Annabi.
0 Response to "Kada kuyi Muqabala da Abdul-jabbar - Kiran Dr. Ahmad Gumi ga Malaman Jihar Kano da gwamnati Kalli Bidiyo anan>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?