Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, -Shawarar kungiyar matasan Arewa ga ‘yan Arewa duba dalili anan
Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya (NYCN) ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake zargin ‘yan Arewa da kai wa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke Oyo,
The Nation ta ruwaito. Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Najeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa 'yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.
A kasuwar ne "inda aka kashe mutane rayuka ko jikkata su, yayin da wasu 'yan daba na Yarbawa suka kone wuraren kasuwanci da motoci.
"Muna yin Allah wadai da wannan harin da kakkausan lafazi sannan kuma muna kira ga jami'an tsaro da su kamo wadanda suka aikata hakan ta yadda za a dakile ayyukan 'yan daba."
Matasan Arewa sun lura da boyayyar manufar da ake da ita na korar ‘yan Arewa mazauna yankin da aka fara tare da yin kira ga dukkan makiyaya da gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, da su bar Mazaunan Gandun Dajin jiharsa. Matasan sun lura:
“Umurnin korar mutanen ya saba wa tanade tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (1999 da aka yi wa kwaskwarima) .
Kundin tsarin mulkin a cewarsu "ya ba da 'yancin yin zirga-zirga ga dukkan ‘yan kasa da kuma 'yancin mallakar kadarori masu motsi da marasa motsi a kowane bangare na kasar.
"Mun yi imanin cewa rashin iyawar gwamnati a dukkan matakai na shawo kan fuka-fukan Sunday Igboho da abokan tafiyarsa ya haifar da ire-irensa.
"Hakan ya jawo, sabbin hare-hare kan 'yan kasuwar da ke zaune da kuma wasu da yawa da ba su iya magana da Yarbanci a Kasuwar Sasha,” in ji sanarwar.
Matasan sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana kungiyar ta Sunday Igboho a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda tunda ba shi da bambanci da Boko Haram.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, -Shawarar kungiyar matasan Arewa ga ‘yan Arewa duba dalili anan"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?