Fati Muhammad ta bayyana dalilinta na barin Kannywood duba dalilin anan
Shahararriyar tsohuwar jarumar nan ta Kannywood, Fati Muhammad ta bayyana abunda ya sa ta barin harkar fim. A cewar jarumar, ta bar fim ne ba wai don ta fi karfin yin sa ba, illa kawai ta ce idan lokacin mutum da shekarunsa suka ja ya kamata ya bar na baya su shigo a dama da su.
A wata hira da tayi da sashin Hausa na BBC Fati ta bayyana cewa a zamanin da take harkar fim, ta fi so a hada ta da shahararren jarumi Ali Nuhu, wanda a cewarta ko yan kallo suna ganin sun fi dacewa da junansu.
Ta kuma bayyana cewa Abida Muhammed ce babbar kawarta wacce a tare suka yi zamani da kuma tashe a masana’antar shirya fina-finan.
Har ila yau, da aka tambaye ta game da wata boyayyiyar baiwa da take da ita, jarumar ta ce a matsayinta na Bafulatana, tana iya kallon saniya ta tsatsi madara daga cikinta sannan ta dafa shi ya zama kindirmo wanda ba kowa ne ya san ta iya hakan ba.
Kan dalilinta na shiga harkar siyasa, Fati ta ce ra’ayi da kaddara ne suka kaita ga shiga lamarin siyasa tare da son mutumin da take goya wa baya wato Alhaji Atiku Abubakar. Ta kuma bayyana cewa abunda ba za ta taba mantawa da shi ba,
shine labarin mutuwarta da aka ta yadawa a lokain da take ganiyar tashe a masana’antar Kannywood, inda tace abun ya taba mata zuciya sosai kasancewar ita ce jaruma ta farko da aka fara yada wannan labarin karyar a kanta.
Daga karshe ta roki Allah ya bata miji na gari domin ta rufa wa kanta asiri sannan ta samu zuri’a dayyiba, a cewarta wannan shine babban burinta a yanzu.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Fati Muhammad ta bayyana dalilinta na barin Kannywood duba dalilin anan "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?