
EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama shugaban jami'ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba kan zargin almundahar kwangilar N260m, The Punch ta ruwaito.
Hukumar ta tsare shi tun ranar Alhamis da ta gabata bayan amsa gayyatar da ta masa don amsa tambayoyi game da zargin amfani da ofishinsa ba yadda ya dace ba, rashawa da almundahar kwangila.
Wata kwakwarar majiya a hukumar yaki da rashawar ta bayyana cewa a shekarar 2018, shugaban jami'ar ya karbi naira miliyan 260 ba bisa ka'ida ba daga hannun wani dan kwangila, Alh. Shehu Sambo, mai kamfanin Ministaco Nigeria Ltd., a kan cewa jami'ar zata bawa kamfaninsa kwangilar naira biliyan 3 don gina katanga.
Sai dai kwangilar ba ta samu ba hakan yasa Sambo ya yi korafi a hukumar yaki da rashawar. Majiyar ta ce, "Har yanzu masu bincike suna yi wa shugaban jami'ar tambayoyi domin suna son sanin abinda ya faru da kudin."
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, a ranar Litinin, ya tabbatar da kama amma shi amma bai bada cikakken bayani ba.
Majiya: Legit.ng
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?