Dakatar da sana'ar Crypto Currency muhimman dalilai da gwamnati ta dogara dasu kafin ta dakatar da kasuwancin
Muhimman bayanai na cigaba da fitowa dangane da dalilan hana cinikayya da sulallan "Crypto" a Nigeria
Hukumar FBI ta kasar Amurka ta ankarar da gwamnatin tarayya cewa ana janye kudade daga kasashen turai tare da shigo da su Nigeria ta hanyoyin damfara
Wata majiya ta bayyana cewa 'yan damfara na shigo da tsakanin $200m zuwa $300m zuwa Nigeria kowanne sati Bayanai na kara fitowa
akan dalilan gwamnatin tarayya na haramta amfani da sulallan yanar gizo yanar gizo da ake kira ''Crypto Currency", ko "Crypto a takaice, wajen duk wata hada-hadar cinikayya.
Babban kasa (CBN) ya fitar da sanarwar hakan a makon da ya gabata inda ya umarci dukkan bankunan da ke fadin kasar nan da su rufe wani asusu da ake amfani da shi wajen harka da ''Crypto''.
Wani rahoto da jaridar Thisday ta wallafa ya bayyana cewa hukumar tsaron kasar Amurka (FBI) ce ta yi wa gwamnatin tarayya korafi akan yadda 'yan Nigeria ke damfarar kasashen turai makudan miliyoyi.
FBI ta sanar da gwamnatin tarayya cewa miliyoyin daloli daga kasashen nahiyar turai na shigowa Nigeria ta barauniya kuma haramtacciyar hanya, wanda hakan kan iya haifar da babbar matsala ga tattalin arfzikin kasa.
Rahoton ya kara bayyana cewa FBI ta nuna cewa 'yan damfara da ake kira ''Yahoo Boys" sun damfari dumbin mazauna kasashen turawan yamma.
A cewar FBI, Yahoo Boys sun yi amfani da salo da dabarun damfara wajen tattare miliyoyin daloli da aka rabawa jama'a a matsayin tallafin annobar korona a kasashen turai tare da shigo da su Nigeria.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, "masu damfarar turawan yamma suna shigo da kudin da yawansu ya kai tsakanin dala miliyan $200 da dala miliyan $300 a kowanne sati, ta hanyar amfani da crypto currency".
"An ankarar da gwamnatin tarayya da CBN akan abubuwan da ke faruwa wanda hakan shine yasa aka dauki matakin gaggawa domin ganin tattalin arzikin kasa bai samu wani lahani ba," kamar yadda Arise News ta rawaito.
Wata babbar matsala ta Crypto, a cewar gwamnatin tarayya, shine yadda yanzu masu garkuwa da mutane suka fara amfani da shi wajen karbar kudin fansa.
Jami'an tsaro suna matakura wahala kafin su iya gano mutumin da ya ajiye kudi ko kuma aka biya shi kudi ta hanyar amfani da Crypto saboda tsananin sirri da boye hanyoyin sauya sulallan zuwa takardu na zahiri bayan sun shiga bankuna.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Dakatar da sana'ar Crypto Currency muhimman dalilai da gwamnati ta dogara dasu kafin ta dakatar da kasuwancin"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?