Daga karshe ankamasu kuma anbasu beli masu Zanga Zangar (End Sars) A Legas Duba dalili
Shahrarren dan wasan barkwanci, Debo Adebayo, wanda aka fi sani da Mr Macaroni ya samu beli tare da sauran mutane 39 da aka kama don suna zanga-zanga a Lekki Toll gate.
Lauyan matasan #EndSARS, Moe Odele, ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita.
"Masu zanga-zangan da aka kama sun samu beli har da Mr Macaroni," Moe Odele ya bayyana. Ta kara da cewa an caji masu zanga-zangan ne kan laifin bada dokokin COVID-19 da kuma saba umurnin haramta yin zanga-zanga. Dukkansu sun ki amincewa da laifin da ake zarginsu dake, lauyan tace.
Kun ji cewa ‘yan sanda a jihar suka kama wasu masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate. Masu zanga-zangar sun mamaye harabar tollgate ne domin yin gangamin kin amincewa da karbo wajen da kamfanin Lekki Concession Company (LCC) tayi.
Idan zaku tuna cewa tollgate ta zamo kara zube ba tare da masu kula da ita ba tun lokacin da lamarin harbi tsakanin rundunar sojin Najeriya da masu zanga-zangar ya wakana a ranar 20 ga watan Oktoba 2020.
Sai dai kuma, a kwanan ne Kwamitin bincike na shari'a kan rikicin #EndSARS ya amince da bukatar kamfanin LCC na karbar ragamar kula da wurin.
Hakan ya fusata masu zanga-zangar #EndSARS lamarin da ya haifar da wani zagaye na zanga-zangar da aka yiwa lakabi da #OccupyLekkiTollGate.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Daga karshe ankamasu kuma anbasu beli masu Zanga Zangar (End Sars) A Legas Duba dalili"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?