Da gaske tsohon Kwamishinan 'yan sandan Kano Muhammad Wakili ya rasu kuwa? Kalli Bidiyon martanin da yayi
Tsohon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano da ke Najeriya CP Muhammad Wakili, ya ƙaryata wasu rahotanni da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa yayin wani hatsarin mota.
Da daren ranar Talata ne wasu labarai da ke bayyana rasuwarsa sakamakon hatsarin mota suka bazu a shafukan sada zumunta, inda mutane suka riƙa sanya hotunansa, suna fatan Allah ya ji ƙansa.
Sai dai yayin zantawa da BBC, CP Muhammad Wakili mai ritaya, ya ce yana nan da ransa, cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
"Ban san ta ina wannan labari ya fito ba, ban san mene ne dalilinsu ba, ban san me suke son su cimma da wannan abu ba, wannan al'amari ya sa mutane damuwa, tun 11 na dare ake ta kira na domin a tabbatar da gaskiyar wannan labari," in ji tsohon kwamishinan 'yan sandan wanda aka fi sani da Singham.
Ya ƙara da cewa ya samu labarin ne sakamakon kiransa da wani babban mutum ya yi, bayan kiciɓis da irin waɗancan labarai da ya yi a shafukan sada zumunta, abin da ya sa hankalinsa ya tashi ya kira wayarsa domin ya tabbatar ko gaskiya ne.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Da gaske tsohon Kwamishinan 'yan sandan Kano Muhammad Wakili ya rasu kuwa? Kalli Bidiyon martanin da yayi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?