Da gaske nake ina sake jaddadawa, ba Buhari ke mulkin kasar nan ba: Inji Farfesa Wole Soyinka
Farfesa Wole Soyinka ya jaddada cewa shi fa bai yarda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar nan ba.
Soyinka ya bayyana hakan yayin jawabi kan matsalar tsaro a wani shirin Arise TV.
Ya ce dubi ga irin abubuwan dake faruwa a fadin tarayya, bai tunanin Buhari ya san abubuwan dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya.
"Na dade ina fadin wannan kuma ina sake jaddadawa, Buhari bai san abubuwan dake faruwa ba. Bai fahimci halin da ake ciki ba," Soyinka yace.
"Saboda a fahimta ta, ba zai yiwu shugaban kasa, shugaban jami'an Sojojin kasa ya ce shi ke jagoranci amma abubuwa su tabarbare haka ba, lallai akwai babban matsala cikin lamarin shugabancin kasar nan."
Wole Soyinka ya yi fashin baki kan rahoton cewa makiyaya sun kai hari gidansa dake jihar Ogun. Ya ce kawai wasu shanu ne suka shiga gidansa kuma ya kore su.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Da gaske nake ina sake jaddadawa, ba Buhari ke mulkin kasar nan ba: Inji Farfesa Wole Soyinka "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?