Da duminsa: Safeton yansanda ya kashe kanshi da bindigarshi
Wani safeton yansanda mai suna inspector Umoh ya kashe kansa ranar Laraba.
Sahara reporters ta ruwaito cewa marigayi Umoh wanda dansandan kwantar da tarzoma ne, ya zo aiki na musamman ne da ake kira special duty a area command na yansanda da ke Birnin Owerri.
Jaridar ta ce Umoh ya koka cewa baya da lafiya. Sai dai babu wanda ya damu. Bayan sun dawo daga aiki ne, sai Unoh ya shiga wani ofis ya rufe kofa, daga bisani sai aka ji karar bindiga.
Jin haka ke da wuya, sai sauran yansanda suka ruga zuwa wannan ofis, amma suka tarar da kofa a rufe daga ciki. Yansandan sun balle kofa, sai dai inspector Umoh ya mutu, Yana kwance a cikin jini bayan ya harbi kanshi a ciki
Kakakin yansandan jihar Imo Orlando Ikeokwu ya tabbatar ma wakilin Jaridar The Nation da faruwar lamarin. Ya ce kwamishinan yansandan jihar Imo CP Nasiru Muhammed ya bayar da umarnin gudanar da bincike.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Da duminsa: Safeton yansanda ya kashe kanshi da bindigarshi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?