--
Da duminsa: Gwamnatin Jihar kano ta saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano duba ranar da aka tsayar anan>>>

Da duminsa: Gwamnatin Jihar kano ta saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano duba ranar da aka tsayar anan>>>




Labari da muke samu a yanzu shine cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya ranar Lahadi, 7 ga watan Maris, a matsayin ranar yin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma malaman jihar.


Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa kwamishinan Yada Labaran Kano, Muhammad Garba da kuma takwaransa na Ma’aikatar Harkokin Addini, Dokta Muhammad Tahir, sun tabbatar da hakan. 


Kwanaki  Shafin Jaridar Legit.ng ya rawaito cewa za a zauna ayi baja-kolin hujjoji da dalilan addini tsakanin Abduljabar Nasiru Kabara da sauran manyan Malaman Kano na Ahlul-Sunnah. 


Abdullahi Ganduje ya shirya taron muhawara a tsakanin Abduljabbar Nasiru Kabara, da sauran Malamai domin a samu fahimtar juna tsakanin wadannan bangarori. Hakan na zuwa ne bayan an yi ta neman gwamnati ta yi na'am da zaman mukabala irin haka. 


A gefe guda kuma, babban malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa game da sabanin da aka samu da Abduljabbar Nasiru Kabara. Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya fito ya yi kira ga gwamnatin Kano da malaman Ahul-Sunnah da su guji yin mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara. 


Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da wani karatun fiqihu a garin Kaduna. 



0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin Jihar kano ta saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano duba ranar da aka tsayar anan>>>"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?