
Da duminsa: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara
Rahotanni na nuna cewa za a saki wasu daga cikin 'yan bindigan da ke hannun hukuma a matsayin wani bangaren na yarjejeniyar sako yaran makarantar Kagara da ma'aikatan da aka yi garkuwa da su.
Kamar yadda The Punch ta wallafa, 'yan bindigan da suka sace yaran suna bukatar a sakar musu 'yan uwansu da ke hannun jami'an tsaro kafin su sako yaran.
Fitaccen malamin nan na addinin Islama mazaunin Kaduna, Ahmad Gumi ya sanar a ranar Juma'a cewa ya samu ganawa da 'yan bindigan jihar Neja a cikin kokarinsu na karbo wadanda aka sace.
A yayin jawabi a kan abinda 'yan bindigan ke bukata kafin su saki yaran, Gumi ya ce: "Basu bada takamaiman sharadin da zai sa su saki daliban ba.
Muna ta dai rokonsu da su sako su amma sun ce za su sako su. "Mun gano cewa suna son a sako mutanensu da aka kama kafin su sako wadanda ke hannunsu."
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Da duminsa: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?