--
Da akwai yiwuwar 'yan Shi'a zasu gwangajeta da sabuwar mota dalleliya kyauta Duba dalili

Da akwai yiwuwar 'yan Shi'a zasu gwangajeta da sabuwar mota dalleliya kyauta Duba dalili


Wani 'Dan Shi'a Mai Amfani da sunan: Habibu Rabiu Nasrallah Ya wallafa a shafinsa na facebook cewa: 

Nayi Takaicin Zagi Da Cin Mutuncin Da Akayiwa Wata Yar Film Me Suna Malama Aisha Dan Kawai ta Taya Musulmi Murnar Zagayowar Watan Da Aka Haifi Sayyadi Ali (As) _Inji Habibu Rabiu Nasrallah.


Inda Yaci Gaba da Cewa:-


"Ina masoya manzan Allah (sawa) da a halin gidansa da Sahabban da suka bishi da gaskiya ya kamata agwan_gwaje wanan yar film  da dalleleyar mota, domin farinciki Ranar da aka haifi sayyadina Ali (as) in yaso masu Zaginta da tsine mata su mutu da bakin Ciki.


Inama dai inada Wannan Halin....😭😭??



Ga Sauran masoya kuma ina fatan Zaku mata addua Allah yasa darajan wanna abu da tayi Allah ya bata gidan aljanna ya kuma kareta daga sharrin masu sharri.


Idan Zaku tuna a ranar 13ga Watan Rajab yayi daidai da Ranar Da Aka Haifi Sahabin Manzan Allah (S) Wato Sayyidina Ali (R.A), 


Wanda Hakan Yasanya wata jaruma kuma wadda tauraruwarta take haskawa a halin yanzu mai Suna Aisha Izzarso Tayi Post A Shafinta Instagram Inda Ta Wallafa Cewa tana taya Daukacin Al-ummar Musulmi Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Sahabin Annabi (S), 


Wanda Hakan Ya Tayar Da Kura Inda Ta Samu Yabo Da Suka Daga Bangarori Daban daban inda wasu ke tayata murnar wasu kuma ke zaginta,  suna zarginta da kasancewa daya daga cikin masu akidar shi'a,  


Inda kuma ita ta sake wallafawa a shafin nata na Intagram Tana Mai nuna damuwarta akan zagin da sukayi mata,  


Ku kalli Bidiyon Anan: 



 

0 Response to "Da akwai yiwuwar 'yan Shi'a zasu gwangajeta da sabuwar mota dalleliya kyauta Duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?