--
Budurwa ta kammala jami'a, ta wallafa hotunanta  soshiyal media jama'a na tayata murna

Budurwa ta kammala jami'a, ta wallafa hotunanta soshiyal media jama'a na tayata murna


Yan Najeriya sun kwararawa wata budurwa sakonnin taya murna ga kyakkyawar budurwa yar Arewa bisa nasaran da ta samu. Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi sanarwa a shafin Tuwita bisa kammala karatun digirinta a fannin karatun lauya. 


Maryam, wacce bata bayyana jami'ar da ta kammala ba ta godewa Allah bisa nasarar da ta samu. Yan Najeriya sun jinjina mata bisa irin kyawun da Allah ya bata yayinda wasu ke taya ta murnan kammala karatunta. 


Budurwar ta bayyana hotunanta sanye da kayan lauyoyi. Hakazalika wasu sun bata shawari kan rayuwa bayan karatu.


@AliyuIbrahimA13 yace: "Ina tayaki murna Barista. ina bukatar kyakkyawar lauya irinki, wacce za ta iya rikita Alkali." 


@Mushin24789 yace; "Ki kasance mai gaskiya duk inda kika samu kanki kuma kada kiyi rashin adalci a aiki..." 

@Omacares1 yace: "Allah ya cigaba da kare ki da shiryar dake hanya madaidaici bisa wannan babban nasara." A bangare wata matashiyar budurwa a kafar sada zumuntar zamani ta twitter mai amfani da suna 


@ButterBibi ta janyo cece-kuce bayan ta bayyana tsabar soyayyarta ga mawaki Don Jazzy. A wasikar da budurwar ta rubuta, ta lissafo jerin nagartattun halayen mawakin da yasa take son shi. 


Ta yi dogaro da karamcinsa, kyawunsa da kuma yadda yake mutunta jama'a a matsayin abubuwan da suka sa take kaunarsa.



0 Response to "Budurwa ta kammala jami'a, ta wallafa hotunanta soshiyal media jama'a na tayata murna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?