
Bayan shan maganin gargajiya yara biyu sun mutu mahaifiyarsu na kwance a asibiti ahalin yanzu,
Yara biyu, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar, sun mutu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu
Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, tana asibiti rai a hannun Allah, likitoci suna ta kokarin ganin sun ceto rayuwarta
Wannan lamarin ya faru ne a ranar Talata a Kwarin Barke dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano Wasu yara 2,
Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar sun rasa rayukansu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu
Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, yanzu haka bata san inda kanta yake ba, likitoci suna iyakar kokarin ganin sun ceto rayuwarta a asibiti.
Al'amarin ya faru ne a ranar Talata a Kwarin Barke dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.
Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa ya ce bayan 'yan sanda sun yi bincike ne suka ga wata gora cike da wani maganin gargajiya da wata gorar koko a gefen gawawwakin a dakin da aka same su.
A cewarsa, maganin gargajiyan da suka sha ne yayi ajalinsu kuma ya sanya mahaifiyarsu a mawuyacin hali. Ya kara da cewa an kai gawawwakin asibiti don binciko asalin silar mutuwarsu.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Bayan shan maganin gargajiya yara biyu sun mutu mahaifiyarsu na kwance a asibiti ahalin yanzu, "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?