
Auren mata fiye da ɗaya yana da kyau - Cewar 'Dan Gwamnan Jihar Kaduna Bayan ya wallafa Hotunan Mahaifinsa da matansa
Dan Gwamna Nasir El-Rufai, Mohammed, a ranar Juma’a, 19 ga Fabrairu, ya saka hotunan matan mahaifinsa a Twitter.
Yaron ya yaba wa auren mata fiye da ɗaya a matsayin abu mai kyau. A cikin hoton, gwamnan ya tsaya a bayan matasan yana mai murmushi da annashuwa.
Da yake wallafa hoton a kan manhajar mai alamar tsuntsun, Mohammed ya ce: "Auren mace fiye da daya yana da kyau.
Na gabatar da iyayena mata!" Mutane da yawa sun yi sharhi kan wallafar, inda hoton ya samu ‘like’ kusan 4,000 a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Kalli wallafar tasa a kasa:
Polygamy is beautiful. I present my mothers! pic.twitter.com/YBxjWCnXtA
— Mohammed El-Rufai (@B_ELRUFAI) February 19, 2021
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Auren mata fiye da ɗaya yana da kyau - Cewar 'Dan Gwamnan Jihar Kaduna Bayan ya wallafa Hotunan Mahaifinsa da matansa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?