Ankama Wani soja ya sayarwa da dan fashi bindigarsa kirar AK-47 duba adadin kudin daya siyar masa kasha mamaki
Wani matashi dan shekara 34 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, Sampson Ebiowei, ya bayyana cewa ya samu bindigarsa ta AK-47 ne daga hannun wani sojan Najeriya da ke aikin Operation Lafiya Dole a yankin Arewa maso Gabas.
Ya kuma kara da cewa sojan ya sayar masa da bindigar ne kan kudi N300,000, Sahara Reporters ta ruwaito.
Ebiowei, wanda ya fito daga Ofunama a karamar hukumar Ovia South West West na jihar Edo, ‘yan sanda sun cafke shi da bindiga da kuma alburusai 88.
Ebiowei ya bayyanawa 'yan sanda cewa ya samu bindigar ne kuma ya fara harkar satar mutane bayan da aka cire sunansa daga jerin wadanda ke cin gajiyar Shirin Afuwa na gwamnatin Niger-Delta na 'yan ta’addan da suka tuba.
Ebiowei, wanda ke da mata uku da yara hudu, ya ce, “An sanya ni ne a cikin shirin afuwa na Gwamnatin Tarayya a da, kuma ana biyana N65,000 a kowane wata, amma kawuna da ya taimake ni na samu aikin ya ce yana son zai ke karbar N20,000 daga cikin kudin.
“Sai dai, saboda na ce a’a, ya cire sunana daga shirin. “Cikin fushi, na tuntubi wani soja da abokina da ke aiki a Maiduguri wanda ya sayar mini da bindigar a kan N300,000 tare da harsasai 88. Na sayi bindigar ne don yaki da kamfanonin mai a wurinmu, saboda sun ki ba mu aiki.”
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Philip Ogbadu, wanda ya gabatar da Ebiowei tare da sauran wadanda ake zargi 11 da sace mutane.
A cewar Ogbadu, rundunar za ta hada kai da mafarautan yankin, ‘yan banga, da kuma hukumomin 'yan uwa don kawo karshen aikata laifuka a jihar.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
Yakamata gwamnati ta dauki matakin kasa ga Yan ta addar da aka Kama aka tabbatar da laifinsu, ba zaman gidan yari ba.
ReplyDelete